• Waƙa ta 136 da Addu’a

 • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 • Albarkar Kasancewa Marasa Aure”: (minti 10)

  • 1Ko 7:32​—Kiristoci marasa aure za su iya ƙara himma a bautarsu ga Jehobah domin ba su da ɗawainiya kamar ma’aurata (w11 1/15 17-18 sakin layi na 3)

  • 1Ko 7:​33, 34​—Kiristoci ma’aurata suna damuwa “da abubuwan duniya” (w08 7/15 27 sakin layi na 1)

  • 1Ko 7:​37, 38​—Kirista da bai yi aure ba don yana son ya ƙara ƙwazo a bautarsa ga Jehobah zai yi hakan fiye da wanda ya yi aure (w96 11/1 5 sakin layi na 14)

 • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

  • 1Ko 7:11​—Wane yanayi ne zai iya sa Kiristoci ma’aurata su rabu? (lv rataye da ke shafi na 220 sakin layi na 2 zuwa shafi na 221)

  • 1Ko 7:36​—Me ya sa ya kamata Kirista ya wuce lokacin da sha’awar jima’i take da ƙarfi sosai kafin ya yi aure? (mwbr19.04-HA an ɗauko daga w00 7/15 31 sakin layi na 2)

  • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?

  • Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?

 • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) 1Ko 8:​1-13 (th darasi na 5)

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

 • Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa: (minti 10) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace, kuma ku tattauna darasi na 4 na ƙasidar nan Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa.

 • Jawabi: (minti 5 ko ƙasa da hakan) w12 11/15 20​—Jigo: Waɗanda Suka Zaɓi Su Kasance Marasa Aure Sun Samu Baiwa Na Yin Hakan Ta Hanyar Mu’ujiza Ne? (th darasi na 12)

RAYUWAR KIRISTA

 • Waƙa ta 37

 • Ka Ji Daɗin Bauta wa Jehobah Ko da Ba Ka Yi Aure Ba: (minti 15) Ku kalli bidiyon. Sa’an nan ka yi waɗannan tambayoyin: Waɗanne ƙalubale ne Kiristoci marasa aure suke fuskanta? (1Ko 7:39) Ta yaya ’yar Yefta ta kafa mana misali mai kyau? Ta yaya Jehobah yake albarkar waɗanda suke bauta masa da dukan zuciyarsu? (Za 84:11) Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su iya taimaka wa ’yan’uwa marasa aure? Mene ne Kiristoci marasa aure za su iya yi don su ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah?

 • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 5 sakin layi na 18-22 da Taƙaitawar da ke shafi na 60-61 da kuma Ƙarin Bayani na 16

 • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

 • Waƙa ta 42 da Addu’a