3:​1-5

Me ya sa abin da malaman addinin Yahudawa suka yi ya sa Yesu baƙin ciki? Domin sun sa dokokin Assabacin sun kasance da wuyan bi ta wurin ƙara wasu dokoki da ba su da muhimmanci. Alal misali, an hana kashe kowane irin ƙwari a ranar Assabaci. An hana warkar da mara lafiya, sai dai idan mara lafiyar yana bakin mutuwa. Hakan yana nufin cewa idan mutum ya ƙarya kashinsa ko kuma ya gurɗe, ba za a yi masa aiki ba sai washegari. Hakika, malaman addinin ba su damu da wahalar da mutumin nan da hannunsa ya shanye yake sha ba.