Sa’ad da Bulus da Sila suke kurkuku, sun rera waƙoƙin yabo ga Allah. (A. M. 16:25) A zamaninmu ma, ’yan’uwanmu sun rera waƙoƙin Mulki sa’ad da suke fursuna a Saiberiya da kuma ƙasar Jamus. Misalinsu ya nuna cewa waƙoƙi suna iya sa Kiristoci su yi ƙarfin hali sa’ad da suke fuskantar tsanantawa.

Nan ba da daɗewa ba, yaruka da yawa za su sami sabon littafin waƙa mai jigo “Sing Out Joyfully” to Jehovah. Idan mun karɓi littafin, za mu iya koyan waƙoƙin sa’ad da muke ibada ta iyali. (Afi 5:19) Ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu tuna da su sa’ad da muke fuskantar tsanantawa. Waƙoƙin Mulki za su taimaka mana mu mai da hankali ga begenmu. Za su iya sa mu yi ƙarfin hali a lokacin jarrabawa. Kuma sa’ad da muke farin ciki, waƙar za ta sa mu “tada murya da murna” saboda farin cikin da muke ciki. (1Lab 15:16; Za 33:1-3) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu wajen rera waɗannan waƙoƙi na Mulki!

KU KALLI BIDIYON NAN WAƘAR DA TA ƘARFAFA FURSUNONI, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Mene ne ya sa Ɗan’uwa Frost ya rubuta waƙa?

  • Ta yaya waƙar ta sa ’yan’uwan da ke sansanin Sachsenhausen ƙarfin hali?

  • A wane irin yanayi ne waƙoƙin Mulki za su iya ƙarfafa ka?

  • Waɗanne waƙoƙin Mulki ne za ka so ka haddace?