Irmiya ya yi gargaɗi cewa za a halaka Urushalima kamar yadda aka halaka Shiloh

26:6

  • Sanduƙin alkawari yana nuna cewa Jehobah na tare da Isra’ilawa, kuma a dā ana ajiye shi a Shiloh

  • Jehobah ya ƙyale Filistiyawa su kwace Sanduƙin Alkawarin kuma tun daga lokacin ba a sake ajiye shi a Shiloh ba

Firistoci da annabawa da kuma dukan mutanen sun yi barazanar kashe Irmiya

26:8, 9, 12, 13

  • Mutanen sun kama Irmiya don annabcin da ya yi game da Urushalima da kuma haikalin

  • Amma Irmiya bai karaya ba

Jehobah ya kāre Irmiya

26:16, 24

  • Irmiya ya ci gaba da kasancewa da gaba gaɗi kuma Jehobah bai yi watsi da shi ba

  • Allah ya sa Ahikam mai ƙarfin hali ya kāre Irmiya

Da taimakon Jehobah, Irmiya ya yi shekara 40 yana shelar saƙon hukunci