’Yan’uwan da suka daɗe ba su fita wa’azi da kuma halarci taro ba, za su halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu a ranar Talata, 11 ga Afrilu. A dā, su ma suna bauta wa Jehobah amma dalilai dabam-dabam sun sa sun daina, kuma an ambata wasu dalilan a cikin ƙasidar nan Ka Komo ga Jehobah. (Ibr 12:1) Duk da haka, Jehobah yana daraja irin waɗannan ’yan’uwan da ya fansa da jinin Ɗansa. (A. M. 20:28; 1Bi 1:18, 19) Ta yaya za mu iya taimaka musu su komo ga Jehobah?

Kamar yadda makiyayi yake neman tumakin da ya ɓata, hakan ma dattawan ikilisiya suke neman irin waɗannan ’yan’uwan don su taimaka musu. (Lu 15:4-7) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunar mu sosai. (Irm 23:3, 4) Dukanmu za mu iya ƙarfafa waɗannan mutanen ba dattawa kawai ba. Ƙoƙarin da muke yi wajen nuna alheri da kuma ƙauna ga ’yan’uwan nan yana faranta wa Jehobah rai kuma yana kawo albarka sosai. (Mis 19:17; A. M. 20:35) Don haka, ka yi tunanin wanda za ka iya ƙarfafa kuma ka yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba!

KU KALLI BIDIYON NAN, KU ƘARFAFA YAN’UWAN DA SUKA DAINA WA’AZI, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Mene ne Abbey ta yi sa’ad da ta haɗu da wata Mashaidiyar da ba ta sani ba?

  • Me ya sa yake da kyau mu gaya wa dattawa idan muna so mu taimaka wa wani da ya daɗe bai fita wa’azi ba?

  • Ta yaya Abbey ta yi shiri sa’ad da take so ta sake ziyarar Laura?

  • Ta yaya Abbey ta nuna naciya da haƙuri da kuma ƙauna sa’ad da take ƙarfafa Laura?

  • Mene ne za mu iya koya daga kwatancin Yesu a Luka 15:8-10?

  • Wane sakamako aka samu sa’ad da yan’uwa suka taimaka wa Laura?