Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ana wa wata ’yar’uwa maraba zuwa Majami’ar Mulki

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Afrilu 2017

Gabatarwa

Yadda za a iya ba da mujallar Awake! da kuma koyar da gaskiya game da Mulkin Allah. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ka Bar Jehobah Ya Gyara Tunaninka da Halayenka

Jehobah yana gyara halayenmu, amma muna bukatar mu dauki mataki.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Marabce Su da Kyau

Ya kamata duk mutumin da ya halarci taronmu ya ga cewa muna kaunar juna sosai. Ta yaya za mu saka hannu wajen tabbatar da cewa hakan ya faru a Majami’unmu?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Kana da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?

A littafin Irmiya sura 24, Jehobah Allah ya kwatanta mutane da baure. Su wane ne suke kama da baure mai kyau kuma ta yaya za mu iya bin misalinsu?

RAYUWAR KIRISTA

Ku Karfafa ’Yan’uwan da Suka Daina Wa’azi

’Yan’uwan da suka daina fita wa’azi har ila suna da tamani a gaban Jehobah. Ta yaya za mu taimaka musu su koma ga Jehobah?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ka Yi Karfin Hali Kamar Irmiya

Irmiya ya yi shekara 40 yana shelar sakon hukunci game da Urushalima. Mene ne ya taimaka masa ya yi karfin hali?

RAYUWAR KIRISTA

Wakokin Mulki Suna Sa Mu Yi Karfin Hali

Rera wakokin mulki ta karfafa Kiristocin da suke fursuna na Sachsenhausen. Wadannan wakokin za su iya sa mu yi karfin hali sa’ad da muke fuskantar tsanatawa.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Jehobah Ya Yi Sabon Alkawari

A wace hanya ce sabon alkawari ya yi dabam da alkawari bisa doka, kuma yaya za mu samu rai na har abada ta wurin sa?