Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Afrilu 2016

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 16-20

Ka Karfafa Wasu da Furuci Mai Kyau

Ka Karfafa Wasu da Furuci Mai Kyau

Ya kamata furucin mai ba da shawara ya zama mai ban ƙarfafa

16:4, 5

  • Ayuba ya bukaci taimako da kuma ƙarfafawa domin ya yi baƙin ciki da kuma sanyin gwiwa

  • Abokan Ayuba uku ba su ƙarfafa shi ba. Maimakon haka, sun zargi Ayuba kuma hakan ya daɗa sa shi baƙin ciki

Baƙar maganar da Bildad ya yi wa Ayuba ta sa shi kuka

19:2, 25

  • Ayuba ya roƙi Allah ya sauƙaƙa matsalolinsa, ko da zai mutu

  • Ayuba ya mai da hankali a kan begen tashin matattu kuma hakan ya sa ya ci gaba da jimrewa