Ƙauna ga Allah da maƙwabtanmu tana mana ja-gora a lokacin taron yanki da kuma sauran lokuta. (Mt 22:37-39) Littafin 1 Korintiyawa 13:4-8 ya ce: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, . . . ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna, . . . ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.” Yayin da kake kallon bidiyon Tunasarwa Game da Taron Yanki, ka yi tunani a kan hanyoyin da za ka iya nuna ƙauna ga wasu a wurin taron.

TA YAYA ZA MU NUNA ƘAUNA . . .

  • sa’ad da muke neman wurin zama?

  • sa’ad da za a soma sauti?

  • a masaukin da aka ba mu?

  • sa’ad da muke taimakawa wajen yin wasu ayyuka?