Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 45-51

Jehobah Ba Zai Yasar da Mai Karyayyar Zuciya Ba

Jehobah Ba Zai Yasar da Mai Karyayyar Zuciya Ba

Dauda ya rubuta Zabura ta 51 bayan da annabi Nathan ya yi masa gargaɗi don zunubin da ya yi da Bath-sheba. Zuciyar Dauda ta dame shi sosai shi ya sa ya faɗi laifinsa.—2Sa 12:1-14.

Ko da yake Dauda ya yi zunubi, amma ya sake ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah

51:3, 4, 8-12, 17

  • Zunubin da Dauda ya yi ya sa shi baƙin ciki sosai shi ya sa ya tuba kuma ya faɗi laifinsa

  • Ya yi baƙin ciki sosai don zunubin da ya yi kuma hakan ya sa ya ji kamar mutumin da aka kakkarya ƙasusuwansa

  • Ya so Allah ya gafarta masa kuma ya sake ƙulla dangantaka da Jehobah don ya sami kwanciyar hankali da yake da shi a dā

  • Ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya riƙa yin biyayya

  • Ya tabbata cewa Jehobah zai gafarta zunubansa