Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Yuni 2016

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 34-37

Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Nagarta

Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Nagarta

“Kada ka . . . ji kishin masu-aika rashin adalci”

37:1, 2

  • Kada ka ƙyale nasara na ɗan lokaci da miyagu suke yi ya janye hankalinka daga bautar Jehobah. Ka mai da hankali ga maƙasudanka da kuma albarkar da Jehobah zai yi maka

“Ka dogara ga Ubangiji, ka yi aikin nagarta”

37:3

  • Ka yi imani cewa Jehobah zai taimake ka a duk lokacin da kake shakka ko alhini. Zai taimaka maka ka kasance da aminci

  • Ka kasance da ƙwazo wajen yaɗa bishara ta Mulkin Allah

“Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji”

37:4

  • Ka ƙayyade lokaci don ka riƙa karanta Kalmar Allah kuma ka yi bimbini a kan abin da ka karanta domin ka san Jehobah sosai

“Ka danƙa wa Ubangiji tafarkinka”

37:5, 6

  • Ka yi imani cewa Jehobah zai taimaka maka ka magance kowace irin matsala

  • Ka nuna hali mai kyau sa’ad da kake fuskantar hamayya da tsanantawa ko kuma aka yi maka sharri

“Ka natsu a gaban Ubangiji, ka yi haƙuri, ka jira shi”

37:7-9

  • Ka guji ɗaukan mataki da garaje domin hakan zai iya jawo maka taƙaici da kuma matsaloli a ibada

“Masu-tawali’u za su gāji ƙasan”

37:10, 11

  • Ka kasance da tawali’u kuma ka jira Jehobah ya cire dukan rashin adalcin da kake fuskata

  • Ka goyi bayan ’yan’uwa Kiristoci kuma ka ƙarfafa masu baƙin ciki cewa Allah zai yi amfani da aljanna wajen cire matsalolinsu

Sarautar Almasihu za ta kawo albarka sosai a duniya