Dauda ya fuskanci matsaloli sosai a rayuwarsa. A lokacin da aka rubuta Zabura 55, ya yi fama da . . .

  • Raini

  • Tsanani

  • Baƙin Ciki don Zunubinsa

  • Masifa Daga Iyalinsa

  • Ciwo

  • Cin Amana

Dauda ya jimre matsalolin da ya fuskanta ko da yake hakan bai kasance masa da sauƙi ba. Shi ya sa aka hure shi ya gaya wa waɗanda suke fuskantar irin yanayin da ya fuskanta cewa: “Ku zuba nawayarku bisa Ubangiji [Jehobah].”

Wane darasi za mu koya daga wannan ayar?

55:22

  1. Ka yi addu’a ga Jehobah sa’ad da kake fuskantar wata matsala ko kuma kana baƙin ciki

  2. Ka nemi ja-gora daga Littafi Mai Tsarki da kuma ƙungiyar Jehobah

  3. Ka yi iya ƙoƙarinka don ka bi da yanayin bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki