Zabura ta 52-59 ta nuna yadda Dauda ya ji sa’ad da yake fuskantar ƙalubale a rayuwarsa. Duk da haka, ya dogara ga Jehobah a waɗannan mawuyacin lokaci. (Za 54:4; 55:22) Ya kuma yabi Jehobah domin maganarsa. (Za 56:10) Shin muna da irin wannan bangaskiya da kuma dogara ga Allah? Shin muna barin Kalmarsa ta yi mana ja-gora sa’ad da muke yanayi mai wuya? (Mis 2:6) Wace aya ta Littafi Mai Tsarki ce ta taimaka maka sa’ad da kake . . .

  • sanyin gwiwa ko baƙin ciki?

  • rashin lafiya?

  • wani ya yi maka laifi?

  • aka tsananta maka?