Massimo Tistarelli mai kera na’ura ne da ke aiki da kansa amma ya fi kwarewa wajen yin amfani da kwamfuta don ya kera na’ura su rika gane abubuwa kamar mutane. Yadda yake daraja kimiyya ya sa ya soma shakkar imaninsa game da juyin halitta.