Wani saurayi ya fara cudanya da wadanda halayensu da rayuwarsu suka bambanta da irin tarbiyyar Kirista da aka yi masa. Sa’ad da ya fara nuna halayen banza, mene ne iyayensa da dan’uwansa suka yi? Wadanne darussa ne za mu iya koya daga wannan wasan da ke dauke da hadarurruka na ainihi da matasa suke fuskanta a yau?