Ko da yake dattijon da yake ba Byong Soo shawara matashi ne, Byong Soo ya samu karfafa don ya karbi shawarar. Ya yi hakan don ya sani cewa Jehobah ne yake amfani da dattijon wajen ba da shawarar.