Kusan shekaru 2,000 da suka shige, an umurci Kiristoci su ‘kaunaci dukan ’yan’uwa.’ Ta yaya Shaidun Jehobah suke bin wannan umurnin? Wannan bidiyon ya nuna hanyoyi uku da ’yan’uwantakarmu take cika wannan umurnin: na 1) ta aikin wa’azi, na 2) ta taimaka wa wadanda suke da bukata, da na 3) ta yin taro don bauta wa Jehobah Allah.