Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 96

Kalmar Allah Tana da Daraja

Ka Zabi Sauti
Kalmar Allah Tana da Daraja
DUBA

(Misalai 2:1)

 1. 1. Kalmar Jehobah Allah Maɗaukaki,

  Ta sa mu san game da nan gaba.

  Saƙonta tana canja halayenmu,

  Tana kwantar mana da rai sosai.

  Jehobah ne Mawallafin littafin

  Don shi ne ya sa a rubuta shi.

  Ruhu mai tsarki ne ya taimake su,

  Mutanen na ƙaunar Allah sosai.

 2. 2. Jehobah ne Mahaliccin duniya,

  Da kuma sama, har da dabbobi.

  Da farko mutane kamiltattu ne

  Amma ba su saurari Allah ba,

  Don Shaiɗan ya yaudari iyayenmu

  Ya yi ƙarya a kan Maɗaukaki.

  Shi ya sa mutane suke wahala.

  Jim kaɗan Allah zai hallaka shi.

 3.  3. Yanzu muna lokacin farin ciki

  Domin Yesu ya zama Sarkinmu.

  Shi ya sa muke yin wa’azin Mulki,

  Don mutane su bauta wa Allah.

  Yesu zai sa mu ji daɗin aljanna,

  Hakan yana ƙarfafa mu sosai.

  Kalmar Jehobah tana amfanar mu,

  Kowace rana mu karanta ta.

(Ka kuma duba 2 Tim. 3:16; 2 Bit. 1:21.)