Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 92

Wurin da Muka Gina Don Sunanka

Ka Zabi Sauti
Wurin da Muka Gina Don Sunanka

(1 Labarbaru 29:16)

 1. 1. Gata ne babba, ya Jehobah,

  Mu gina maka gidan nan!

  Muna miƙa maka shi duka

  Domin a yabe ka sosai.

  Dukan abin da muka ba ka,

  Ai naka ne tun asali.

  Kuzarinmu da dukiyarmu,

  Mun miƙa su, Ya Jehobah.

  (AMSHI)

  Yanzu bari mu miƙa ma,

  Gidan nan don ibada.

  Mun keɓe maka gidan nan,

  Ya Uba ka karɓe shi.

 2. 2. Bari mu ɗaukaka Jehobah,

  Don ikonsa da ƙaunarsa.

  Muna roƙo ka ji addu’ar

  Masu so su san Kalmarka.

  Kai muka gina wa gidan nan,

  Duk za mu kula da gidan.

  Mun san cewa zai ba da Shaida

  Ga sunanka, Ya Jehobah.

  (AMSHI)

  Yanzu bari mu miƙa ma,

  Gidan nan don ibada.

  Mun keɓe maka gidan nan,

  Ya Uba ka karɓe shi.

(Ka kuma duba 1 Sar. 8:​18, 27; 1 Laba. 29:​11-14; A. M. 20:24.)