WAƘA TA 91
Aikin da Muka Yi Don Muna Kaunar Allah
(Zabura 127:1)
1. Jehobah Maɗaukaki,
Muna matuƙar godiya
Domin ka yi mana albarka
A ayyukanmu!
Gina maka gidan nan,
Babban gata ne fa sosai.
Ga shi mun kammala ginin nan
Da taimakonka.
(AMSHI)
Mun gode Allahnmu Jehobah
Don ginin nan da muka yi.
Muna roƙo ka taimake mu don mu riƙa
Bauta maka har abada.
2. Mun yi cuɗanya sosai
Da ’yan’uwa ƙaunatattu!
Ba za mu manta da ’yan’uwan
Duk rayuwarmu!
Allah ya taimake mu,
A ayyukan da muka yi.
Mun kuma tsarkake sunanka,
Mun gode sosai!
(AMSHI)
Mun gode Allahnmu Jehobah
Don ginin nan da muka yi.
Muna roƙo ka taimake mu don mu riƙa
Bauta maka har abada.
(Ka kuma duba Zab. 116:1; 147:1; Rom. 15:6.)