Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 90

Mu Rika Karfafa Juna

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Karfafa Juna

(Ibraniyawa 10:​24, 25)

 1. 1. In muna ƙarfafa ʼyan’uwa

  Don su bauta wa Jehobah.

  ’Yan’uwancinmu zai yi ƙarfi,

  Za mu sami kwanciyar rai.

  Ƙauna tsakaninmu ’yan’uwa

  Na sa mu iya jimrewa.

  Halartan taro da ’yan’uwa,

  Zai sa mu riƙa jimrewa.

 2. 2. Kalmomi masu ban ƙarfafa

  Suna da daɗin ji sosai!

  Muna jin irin kalmomin nan

  Daga wurin ’yan’uwanmu.

  Yin aiki da mutanen Allah,

  Na sa mu yin murna sosai!

  Sai mu riƙa ƙarfafa juna

  Domin mu iya jimrewa.

 3. 3. Da bangaskiya muna ganin

  Ranar Jehobah na zuwa.

  Sai mu riƙa kusantar juna

  Don mu riƙa bauta masa.

  Tare da mutanen Jehobah,

  Za mu bauta wa Allahnmu.

  Za mu riƙa ƙarfafa juna

  Domin mu riƙe aminci.

(Ka kuma duba Luk. 22:32; A. M. 14:​21, 22; Gal. 6:2; 1 Tas. 5:14.)