Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 89

Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

Ka Zabi Sauti
Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka
DUBA

(Luka 11:28)

 1. 1. Mu riƙa saurarar umurnin Kristi,

  Umurnin na nuna mana hanya.

  Za mu yi murna, mu sami albarka,

  In muna bin dukan dokokinsa.

  (AMSHI)

  Za mu sami albarka,

  In mun bi Kalmar Allah.

  Za mu ji daɗin bauta wa Allah.

  Ji, ka sami albarka.

 2. 2. Hali mai kyau zai ceci rayuwarmu,

  Kamar ginin da ke a kan dutse.

  In duk muna bin ja-gorancin Yesu,

  Za mu sami rai na har abada.

  (AMSHI)

  Za mu sami albarka,

  In mun bi Kalmar Allah.

  Za mu ji daɗin bauta wa Allah.

  Ji, ka sami albarka.

 3. 3. Kamar bishiyoyi masu yin ’ya’ya

  Da aka shuka kusa da tafki,

  In muna yin biyayya ga Jehobah,

  Za mu yi rayuwa har abada.

  (AMSHI)

  Za mu sami albarka,

  In mun bi Kalmar Allah.

  Za mu ji daɗin bauta wa Allah.

  Ji, ka sami albarka.

(Ka kuma duba K. Sha. 28:2; Zab. 1:3; Mis. 10:22; Mat. 7:​24-27; Luk. 6:​47-49.)