Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 87

Ku Zo Mu Sami Karfafa!

Ka Zabi Sauti
Ku Zo Mu Sami Karfafa!
DUBA

(Ibraniyawa 10:​24, 25)

 1. 1. Muna cikin zamanin da ʼyan Adam

  Suke cikin duhu sosai.

  Bin umurnin Allah zai taimake mu

  Don kada mu bijire fa.

  Yin taro yana ƙarfafa ƙaunarmu

  Da kuma bangaskiyarmu.

  Yana sa mu yi ayyuka masu kyau,

  Yana sa mu jimre sosai.

  Ba za mu ƙi bin umurnin Allah ba,

  Muna so mu yi nufinsa.

  Yana koya mana nufin Jehobah,

  Yana sa mu so gaskiya.

 2. 2. Jehobah Allah ya san bukatunmu,

  Mu bi mizaninsa sosai.

  Mugun ba zai iya rinjayar mu ba,

  In muna halartan taro.

  Muna koyan abubuwa da yawa

  Daga ƙwararrun ’yan’uwa.

  Dukan ’yan’uwanmu na taimakon mu,

  Mun san ba mu kaɗaita ba.

  Kuma kafin nufin Allah ya cika,

  Mu riƙa halartan taro.

  A taro, Jehobah na koya mana

  Hikima da dokokinsa.

(Ka kuma duba Zab. 37:18; 140:1; Mis. 18:1; Afis. 5:16; Yaƙ. 3:17.)