Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 81

Rayuwar Majagaba

Ka Zabi Sauti
Rayuwar Majagaba
DUBA

(Mai-Wa’azi 11:6)

 1. 1. Gari na wayewa kafin a yi rana,

  Ko da muna jin barci

  za mu fita yin wa’azi.

  Muna yin fara’a ga mutanen yankin.

  Muna dagewa ko

  da suna saurara ko a’a.

  (AMSHI)

  Mu muka yi zaɓin,

  Mu bayin Allah ne,

  Duk abin da ya ce za mu yi.

  Ko da me ya faru

  Za mu yi wa’azi.

  Ta hakan za mu nuna masa: “Ƙaunarmu.”

 2. 2. Sa’ad da mun dawo da faɗuwar rana,

  Mun gaji, duk da haka

  muna farin ciki sosai.

  Muna ƙoƙartawa, muna son hidimar.

  Mun gode wa Allah

  domin yana mana albarka.

  (AMSHI)

  Mu muka yi zaɓin,

  Mu bayin Allah ne,

  Duk abin da ya ce za mu yi.

  Ko da me ya faru

  Za mu yi wa’azi.

  Ta hakan za mu nuna masa: “Ƙaunarmu.”

(Ka kuma duba Josh. 24:15; Zab. 92:2; Rom. 14:8.)