WAƘA TA 80
‘Mu Dandana, Mu Gani, Ubangiji Nagari Ne’
Ka Zabi Sauti
(Zabura 34:8)
1. Muna daraja bautarmu
Da wa’azin da muke yi.
Muna wa’azi da duk ƙarfinmu
Don kowa ya ji saƙonmu.
(AMSHI)
Jehobah ya ce: ‘Mu ɗanɗana
Mu ga duk alherinsa.’
Mu bauta masa da ƙarfinmu,
Zai yi mana albarka.
2. Majagaba ʼyan’uwanmu,
Jehobah zai ƙarfafa ku.
Zai kuma biya duk bukatunku,
Ba zai yi watsi da ku ba.
(AMSHI)
Jehobah ya ce: ‘Mu ɗanɗana
Mu ga duk alherinsa.’
Mu bauta masa da ƙarfinmu,
Zai yi mana albarka.
(Ka kuma duba Mar. 14:8; Luk. 21:2; 1 Tim. 1:12; 6:6.)