WAƘA TA 73
Ka Ba Mu Karfin Zuciya
-
1. Muna yin wa’azin Mulki,
Muna shelar sunanka.
Maƙiyanmu ba sa son mu,
Suna tsananta mana.
Amma ba ma tsoron su,
Kai za mu yi wa biyayya.
Ka ba mu ruhunka mai tsarki
Ya Jehobah, ji roƙonmu.
(AMSHI)
Ya Uba ka taimake mu
Mu yi ƙarfin zuciya.
Don mu riƙa yin wa’azi
Muna gaya wa kowa,
Armageddon fa ya kusa,
Kafin a soma yaƙin nan,
Ka ba mu ƙarfin zuciya,
Muna roƙo.
-
2. Don dukanmu ajizai ne
Muna iya jin tsoro.
Mun san za ka taimake mu,
Mun dogara gare ka.
Ka duba wulaƙancin
Da mutane suke mana.
Sai ka riƙa taimaka mana
Don mu yi shelar sunanka.
(AMSHI)
Ya Uba ka taimake mu
Mu yi ƙarfin zuciya.
Don mu riƙa yin wa’azi
Muna gaya wa kowa,
Armageddon fa ya kusa,
Kafin a soma yaƙin nan,
Ka ba mu ƙarfin zuciya,
Muna roƙo.
(Ka kuma duba 1 Tas. 2:2; Ibran. 10:35.)

