Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 72

Mu Yada Gaskiya Game da Mulkin Allah

Ka Zabi Sauti
Mu Yada Gaskiya Game da Mulkin Allah
DUBA

(Ayyukan Manzanni 20:​20, 21)

 1. 1. A dā muna cikin duhu

  Shaiɗan ya makantar da mu.

  Sai Jehobah Allahnmu,

  Ya koya mana gaskiya.

  Mun koyi nufin Allahnmu,

  Mun soma wa’azin Mulki,

  Mun yaɗa ɗaukakarsa

  Kuma muna tsarkake sunansa.

  Muna wa’azi ga kowa,

  Gida-gida da kan titi.

  Kullum muna ƙoƙartawa

  Don mu yi wa’azi sosai.

  Yin wa’azi a ko’ina

  Na sa a bauta wa Allah,

  Mu riƙa ƙoƙartawa

  Har sai Jehobah ya ce ya isa.

(Ka kuma duba Josh. 9:9; Isha. 24:15; Yoh. 8:​12, 32.)