Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 7

Jehobah Ne Karfinmu

Ka Zabi Sauti
Jehobah Ne Karfinmu
DUBA

(Ishaya 12:2)

 1. 1. Allah Jehobah, kai Mai iko ne,

  Kai ke ceto da kiyaye mu fa.

  Mu ne Shaidu, muna yin wa’azi,

  Ko da jama’a sun ji ko sun ƙi.

  (AMSHI)

  Jehobah Allah, kai ne ƙarfinmu,

  Muna yin shelar ɗaukakarka.

  Allah Jehobah, Maɗaukaki ne,

  Mafakarmu da Madogararmu.

 2. 2. Muna alfahari mu naka ne,

  Kuma mun san gaskiyar Kalmarka.

  Mun koyi nufinka a Nassosi.

  Mun ƙudurta yin shelar Mulkinka.

  (AMSHI)

  Jehobah Allah, kai ne ƙarfinmu,

  Muna yin shelar ɗaukakarka.

  Allah Jehobah, Maɗaukaki ne,

  Mafakarmu da Madogararmu.

 3. 3. Allah Jehobah, muna bauta ma.

  Muna yin hakan ko me zai faru.

  Ko da Shaiɗan yana jarabtar mu,

  Za mu dogara da kai koyaushe.

  (AMSHI)

  Jehobah Allah, kai ne ƙarfinmu,

  Muna yin shelar ɗaukakarka.

  Allah Jehobah, Maɗaukaki ne,

  Mafakarmu da Madogararmu.

(Ka kuma duba 2 Sam. 22:3; Zab. 18:2; Isha. 43:12.)