Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 69

Mu Ci Gaba da Yin Wa’azi Game da Mulkin Allah!

Ka Zabi Sauti
Mu Ci Gaba da Yin Wa’azi Game da Mulkin Allah!

(2 Timotawus 4:5)

 1. 1. Mu ci gaba da yin wa’azi

  Ga dukan maƙwabtanmu.

  Mu nuna musu ƙauna sosai,

  Mu sa su san Jehobah.

  Muna murnar yaɗa bishara,

  Don hakan gata ne babba.

  Mu riƙa yin shelar bishara,

  Mu girmama sunan Allah.

  (AMSHI)

  Mu je mu yi wa dukan

  Mutane wa’azin Mulkin.

  Mu ci gaba da riƙe aminci

  ga Maɗaukaki.

 2. 2. Mu tashi mu je yin bishara,

  Bisharar Mulkin Allah.

  Mu matasa da tsofaffi ma,

  Har da dukan shafaffu.

  Dukan mutane na bukatar

  Su ji wa’azin Mulkin nan.

  Jehobah zai taimaka mana,

  Mu yi gaba gaɗi sosai!

  (AMSHI)

  Mu je mu yi wa dukan

  Mutane wa’azin Mulkin.

  Mu ci gaba da riƙe aminci

  ga Maɗaukaki.

(Ka kuma duba Zab. 23:4; A. M. 4:​29, 31.)