Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 68

Mu Taimaki Mutane Su Bauta wa Jehobah

Ka Zabi Sauti
Mu Taimaki Mutane Su Bauta wa Jehobah

(Matta 13:​4-8)

 1. 1. Mu yi aikin Ubangijinmu,

  Mu riƙa bin dokokinsa.

  Ubangiji ne ja-goranmu,

  Zai koya mana hanyarsa.

  Idan muna wa’azin bishara

  Wasu za su saurare mu.

  Don hakan mu yi iya ƙoƙarinmu

  Kuma mu yi wa’azi sosai.

 2. 2. In muna yin shela da himma

  Za mu iya yin nasara.

  Za mu taimaka wa mutane

  Domin su bauta wa Allah.

  Mu kawar da shakkar da suke yi

  Domin su iya jimrewa.

  Za mu yi murna sosai idan mun ga

  Yadda suke samun ci gaba.

(Ka kuma duba Mat. 13:​19-23; 22:37.)