Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 67

Mu Yi “Wa’azin Kalmar Allah”

Mu Yi “Wa’azin Kalmar Allah”

(2 Timotawus 4:2)

 1. 1. Allah ya ba mu umurni,

  Umurnin da ya kamata mu bi.

  Mu riƙa yin shiri a kullum

  Domin mu yi wa’azin bishara.

  (AMSHI)

  Mu yi shela

  Mu gaya wa mutane

  Da ƙwazo!

  Domin ƙarshe na zuwa,

  Yi shela

  Don su juyo ga Allah,

  Yi shela

  A ko’ina!

 2. 2. Tsanantawa har da ƙunci,

  Suna iya hana mu wa’azi.

  Ba za mu rufe bakinmu ba,

  Ko da mutane sun ƙi saurara.

  (AMSHI)

  Mu yi shela

  Mu gaya wa mutane

  Da ƙwazo!

  Domin ƙarshe na zuwa,

  Yi shela

  Don su juyo ga Allah,

  Yi shela

  A ko’ina!

 3. 3. Wasu za su saurare mu,

  Za mu koya musu Kalmar Allah.

  Bishara na sa su yin bege,

  Da kuma tsarkake sunan Allah.

  (AMSHI)

  Mu yi shela

  Mu gaya wa mutane

  Da ƙwazo!

  Domin ƙarshe na zuwa,

  Yi shela

  Don su juyo ga Allah,

  Yi shela

  A ko’ina!

(Ka kuma duba Mat. 10:7; 24:14; A. M. 10:42; 1 Bit. 3:15.)