Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 62

Sabuwar Waka

Ka Zabi Sauti
Sabuwar Waka
DUBA

(Zabura 98)

 1. 1. Mu rera yabo ga Allahn sama mai ƙauna.

  Shela ayyukansa da waɗanda zai yi,

  Yabi ikonsa, shi Allah ne Maɗaukaki.

  Yana yin adalci,

  A duk hukuncinsa.

  (AMSHI)

  Mu rera

  Sabuwar waƙar nan!

  Jehobah

  Ya zama Sarkinmu.

 2. 2. Mu ɗaga murya, mu yabi Allah Sarkinmu!

  Ɗaukaka sunansa da kuma ikonsa.

  Mu rera yabo da dukan zuciyarmu fa.

  Mu busa ƙahoni,

  Mu yabi Jehobah.

  (AMSHI)

  Mu rera

  Sabuwar waƙar nan!

  Jehobah

  Ya zama Sarkinmu.

 3. 3. Dukan halittu da ke teku su yi yabo.

  Halittun duniya, su rera waƙa ma.

  Ƙasa da rafi, duk za su rera ma yabo.

  Duwatsu da tuddai,

  Su ɗaga muryoyi.

  (AMSHI)

  Mu rera

  Sabuwar waƙar nan!

  Jehobah

  Ya zama Sarkinmu.

(Ka kuma duba Zab. 96:1; 149:1; Isha. 42:10.)