Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 58

Muna Neman Mutane Masu Saukin Kai

Ka Zabi Sauti
Muna Neman Mutane Masu Saukin Kai

(Luka 10:6)

 1. 1. Yesu ya ce mu riƙa wa’azi.

  Cikin rana, cikin sanyi,

  Ya yi wa kowa wa’azi.

  Ya yi hakan don yana ƙaunar su.

  Ya yi shela daga safe

  har zuwa yamma.

  Muna zuwa gida-gida

  Domin mu gaya wa kowa

  Allah ya kusan cire wahaloli.

  (AMSHI)

  Muna zuwa

  Yaɗa bisharar Mulkin Allah.

  Muna neman

  Waɗanda ke son samun ceto.

  Fatanmu ne

  Su ji saƙon.

 2.  2. Muna bisharar Mulkin da ƙwazo.

  Maƙwabtanmu, da danginmu,

  Muna so su san gaskiya.

  Ƙauna ce ta sa muke yin hakan,

  Mu riƙa taimakon su,

  su bauta wa Allah.

  Muna shela a ko’ina

  Kuma muna farin ciki,

  Idan mutane na jin wa’azinmu.

  (AMSHI)

  Muna zuwa

  Yaɗa bisharar Mulkin Allah.

  Muna neman

  Waɗanda ke son samun ceto.

  Fatanmu ne

  Su ji saƙon.

(Ka kuma duba Isha. 52:7; Mat. 28:​19, 20; Luk. 8:1; Rom. 10:10.)