Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 57

Ku Yi wa Dukan Mutane Wa’azi

Ka Zabi Sauti
Ku Yi wa Dukan Mutane Wa’azi
DUBA

(1 Timotawus 2:4)

 1. 1. Muna so mu yi koyi da Allah,

  Shi ba ya nuna wa kowa son kai.

  Yana son kowa ya sami ceto,

  Yana son kowa ya bauta masa.

  (AMSHI)

  Muna neman mutane,

  Ba ma duba fuskarsu,

  Abin da Allah yake so ke nan.

  Don yaɗa bisharar nan,

  Muna zuwa ko’ina

  Don mutane su bauta wa Allah.

 2. 2. Za mu yi wa’azi a ko’ina,

  Ko da yaya yanayinsu yake.

  Halinsu ne ke da muhimmanci,

  Jehobah ne ke ganin zucinsu.

  (AMSHI)

  Muna neman mutane,

  Ba ma duba fuskarsu,

  Abin da Allah yake so ke nan.

  Don yaɗa bisharar nan,

  Muna zuwa ko’ina

  Don mutane su bauta wa Allah.

 3. 3. Jehobah na son dukan mutane,

  Su guje wa halin duniyar nan.

  Shi ne ya sa muke yin wa’azi,

  Ga dukan mutanen da za su ji.

  (AMSHI)

  Muna neman mutane,

  Ba ma duba fuskarsu,

  Abin da Allah yake so ke nan.

  Don yaɗa bisharar nan,

  Muna zuwa ko’ina

  Don mutane su bauta wa Allah.

(Ka kuma duba Yoh. 12:32; A. M. 10:34; 1 Tim. 4:10; Tit. 2:11.)