Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 56

Ka Rike Gaskiya

Ka Zabi Sauti
Ka Rike Gaskiya
DUBA

(Misalai 3:​1, 2)

 1. 1. Bauta wa Allah shi ne abu mafi kyau,

  Amma kai ne za ka yi zaɓin.

  Don haka ka bi dukan umurnin Allah,

  Ka nuna aminci sosai.

  (AMSHI)

  Ka bauta masa.

  Ka yi da duk zuciya.

  Jehobah zai yi

  Maka albarka

  In ka riƙe gaskiya.

 2. 2. Duk ƙoƙarinka da ayyukan da ka yi

  A bautar Allah da Mulkinsa,

  Za su sa Allah ya yi maka albarka,

  Ka sami rai har abada.

  (AMSHI)

  Ka bauta masa.

  Ka yi da duk zuciya.

  Jehobah zai yi

  Maka albarka

  In ka riƙe gaskiya.

 3. 3. Mu duka muna kamar ’ya’ya gun Allah,

  Dole mu bi ja-gorancinsa.

  Ka yi tafiya da Ubanmu na sama

  Don ka sami albarkarsa.

  (AMSHI)

  Ka bauta masa.

  Ka yi da duk zuciya.

  Jehobah zai yi

  Maka albarka

  In ka riƙe gaskiya.

(Ka kuma duba Zab. 26:3; Mis. 8:35; 15:31; Yoh. 8:​31, 32.)