Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 54

‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

(Ishaya 30:​20, 21)

 1. 1. Akwai wata hanya,

  Hanyar salama ce.

  An ambata hanyar

  A Kalmar Allahnmu.

  Yesu ya ce mu riƙa

  Bin wannan hanyar.

  Kuma muna cikin

  Wannan hanyar a yau.

  (AMSHI)

  Ga hanyar rai a nan, Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta, kome jarrabawa!

  Allah na kira: ‘Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta domin hanyar rai ce.’

 2. 2. Akwai hanyar ƙauna

  Wadda ba irin ta.

  Nufin Allah shi ne

  Mu bi wannan hanyar.

  Don shi mai ƙauna ne

  Da kuma gaskiya.

  Ku yi tafiya a

  Hanyar ƙaunar nan fa.

  (AMSHI)

  Ga hanyar rai a nan, Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta, kome jarrabawa!

  Allah na kira: ‘Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta domin hanyar rai ce.’

 3. 3. Akwai wata hanya

  Ta rai har abada.

  Allah Jehobah ne

  Ya yi alkawari.

  Babu wata hanya

  Kamar wannan hanyar.

  Jehobah mun gode,

  Ba za mu bar ta ba.

  (AMSHI)

  Ga hanyar rai a nan, Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta, kome jarrabawa!

  Allah na kira: ‘Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta domin hanyar rai ce.’

(Ka kuma duba Zab. 32:8; 139:24; Mis. 6:23.)