Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 53

Muna Shirin Fita Wa’azi

Muna Shirin Fita Wa’azi

(Irmiya 1:17)

 1. 1. Mun tashi

  Za mu fita

  Don mu je yin wa’azi.

  Ana yayyafi,

  Har da sanyi sosai.

  A lokacin ne fa yin barci

  ke daɗi.

  (AMSHI)

  Yin addu’a da kuma shiri

  Da fatan alheri,

  Za su ba mu ƙarfin zuciya

  Da muke so.

  Mala’iku da Yesu Kristi,

  Suna taimakon mu.

  Ga kuma dukan ʼyan’uwanmu,

  Sai godiya.

 2. 2. Za mu yi

  Murna sosai

  In mun bi umurnin nan.

  Allah na ganin

  Dukan ƙoƙarinmu.

  Yana tunawa da ƙaunarmu,

  ba shakka.

  (AMSHI)

  Yin addu’a da kuma shiri

  Da fatan alheri,

  Za su ba mu ƙarfin zuciya

  Da muke so.

  Mala’iku da Yesu Kristi,

  Suna taimakon mu.

  Ga kuma dukan ʼyan’uwanmu,

  Sai godiya.

(Ka kuma duba M. Wa. 11:4; Mat. 10:​5, 7; Luk. 10:1; Tit. 2:14.)