Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 5

Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi

Ka Zabi Sauti
Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi
DUBA

(Zabura 139)

 1. 1. Jehobah Allahnmu mai iko,

  Kana sane da duk ayyukana.

  Kana ganin kome a zuciyata,

  Furucina, halayena,

  duk ka san su.

  Ka ga sa’ad da nake ciki,

  Kafin ma a san za a haife ni.

  Fasalina duk a gabanka suke.

  Ina yabo da kuma son

  ayyukanka.

  Hikimarka tana da ban mamaki,

  Ina farin cikin sanin hakan.

  Idan na ɓoye a inda ba haske,

  Duk da haka Jehobah zai gan ni.

  Jehobah a ina zan ɓoye

  da ba za ka iya gani na ba?

  Ko na shiga Kabari ko a sama,

  ko cikin duhu ko teku,

  za ka gan ni.

(Ka kuma duba Zab. 66:3; 94:19; Irm. 17:10.)