Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 49

Mu Rika Faranta Ran Jehobah

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Faranta Ran Jehobah
DUBA

(Misalai 27:11)

 1. 1. Uba, mun yi alkawari,

  Alkawarin bauta maka.

  Muna so mu yi biyayya

  Domin mu faranta ranka.

 2. 2. Wakilinka a duniya

  Yana yin shelar girmanka,

  Yana ciyar da mu sosai

  Don mu riƙa yin nufinka.

 3. 3. Ka ba mu ruhunka, Allah,

  Domin mu riƙe aminci.

  Hakan zai sa mu yabe ka

  Kuma mu faranta ranka.

(Ka kuma duba Mat. 24:​45-47; Luk. 11:13; 22:42.)