‘KU RERA WAKA DA MURNA’ GA JEHOBAH

Mu Rika Bin Ja-gorancin Jehobah (Waka ta 48)

Hausa
Mu Rika Bin Ja-gorancin Jehobah (Waka ta 48)
/assets/ct/7e6416ec85/images/syn_placeholder_sqr.png
sjj waƙa ta 48

WAƘA TA 48

Mu Rika Bin Ja-gorancin Jehobah

Mu Rika Bin Ja-gorancin Jehobah

(Mikah 6:8)

  1. 1. Za mu riƙa yin tafiya

    Da Jehobah Maɗaukakinmu.

    Allahnmu mai alheri ne

    Yana sāka wa amininsa!

    Jehobah ne ya jawo mu

    Domin mu kusace shi.

    Mun yi alkawari cewa

    Za mu bauta wa Allahnmu.

  2. 2. Shaiɗan maƙiyin Jehobah

    Yana tsananta wa dukanmu,

    Domin Allah ya ƙayyade

    Ranar da za ya halaka shi.

    Jehobah zai taimake mu

    Mu kusace shi sosai,

    Domin mu riƙe aminci

    Mu bi ja-gorancinsa ma.

  3. 3. Jehobah ya yi tanadi,

    Tanadin ruhu da Kalmarsa

    Da kuma ikilisiya

    Da addu’o’in da muke yi.

    In mun bauta wa Jehobah

    Zai riƙa koyar da mu,

    Zai sa mu riƙe aminci,

    Kuma mu faranta ransa.

(Ka kuma duba Far. 5:24; 6:9; 1 Sar. 2:​3, 4.)