Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 45

Abubuwan da Nake Tunani a Kai

Ka Zabi Sauti
Abubuwan da Nake Tunani a Kai

(Zabura 19:14)

 1. 1. Abin da ke zuciyata,

  Abin da nake tunani,

  Bari su faranta ma rai,

  Don in zama amininka.

  Sa’ad da nake damuwa

  Kuma na kasa yin barci.

  Bari in tuna Allahna

  Da abubuwa masu kyau.

 2. 2. Abubuwa masu tsarki,

  Abubuwa na gaskiya,

  Abubuwan da sun dace,

  Za su kwantar mini da rai.

  Ina ƙaunar koyarwarka,

  Kana koyar da ni sosai.

  Bari in tuna Kalmarka,

  In riƙa bin umurninka.

(Ka kuma duba Zab. 49:3; 63:6; 139:​17, 23; Filib. 4:​7, 8; 1 Tim. 4:15.)