Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 43

Addu’ar Godiya

Ka Zabi Sauti
Addu’ar Godiya

(Zabura 95:2)

 1. 1. Allah Jehobah mai amsa addu’a.

  Muna yabon ka da gode maka.

  Mun amince kai ne za mu bauta wa

  Kuma mun san za ka kula da mu.

  Muna kuskure don mu ajizai ne.

  Muna roƙo ka gafarta mana.

  Muna godiya domin ka fanshe mu.

  Kuma ka san yanayinmu sosai.

 2. 2. Muna gode maka domin ƙaunarka.

  Mun gode don muna ƙungiyarka.

  Ka sa mun san ka, ka taimaka mana.

  Ka sa mu riƙa bin umurninka.

  Muna da ruhunka, Allah mun gode.

  Da ƙarfin halin da muke da shi.

  Ka sa mu yi murna a hidimarka.

  Mun gode Allah don alherinka.

(Ka kuma duba Zab. 65:​2, 4, 11; Filib. 4:6.)