Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 42

Addu’ar Bawan Allah

Ka Zabi Sauti
Addu’ar Bawan Allah
DUBA

(Afisawa 6:18)

 1. 1. Mafi Iko, Jehobah Allahnmu.

  Ka tsarkake sunanka mafi girma.

  Kana aikata duk nufinka,

  Muna jiran albarkar Mulkinka.

  Muna jira ya zo don

  Mu sami albarkarsa.

 2. 2. Allah muna godiya don ranmu.

  Ka ba mu abubuwa masu kyau.

  Ka ba mu rai da kuma haske,

  Ka ba mu hikima da basira.

  Muna maka godiya

  Kuma muna yabon ka.

 3. 3. A duniya muna shan wahala.

  Amma muna dogara a gare ka,

  Allah Ubanmu muna roƙo.

  Ka ba mu ƙarfin da za mu jimre

  Kuma mu yi nufinka.

  Mu riƙe amincinmu.

(Ka duba Zab. 36:9; 50:14; Yoh. 16:33; Yaƙ. 1:5.)