Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 4

“Jehobah Makiyayina Ne”

Ka Zabi Sauti
“Jehobah Makiyayina Ne”
DUBA

(Zabura 23)

 1. 1. Jehobah ne Makiyayi,

  Ja-gorancinsa zan bi.

  Shi ne ya san duk tunanina,

  Ya san duk bukatuna.

  Ya kai ni wurin albarka,

  Inda akwai kyau sosai.

  Yana min ja-goranci da ƙauna

  Don in sami salama.

  Yana ja-goranci da ƙauna

  Don in sami salama.

 2. 2. Dokokinka na adalci

  Suna kwantar min da rai.

  Don sunanka ka taimaka min

  In riƙa yin nufinka.

  Ko ina cikin wahala,

  Ka kiyaye ni, Allah.

  Ba zan taɓa jin tsoron kome ba

  Domin kai ne Allahna.

  Ba za ni ji tsoron kome ba

  Domin kai ne Allahna.

 3.  3. Jehobah Makiyayina,

  Ja-gorancinka zan bi.

  Ka ƙarfafa ni, ka kāre ni,

  Ka biya bukatuna.

  Ina dogara gare ka,

  A dukan rayuwata.

  Bari ƙaunarka da kulawarka

  Su bi ni har abada.

  Bari ƙauna da kulawarka

  Su bi ni har abada.

(Ka kuma duba Zab. 28:9; 80:1.)