Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 39

Mu Yi Suna Mai Kyau a Wurin Allah

Ka Zabi Sauti
Mu Yi Suna Mai Kyau a Wurin Allah
DUBA

(Mai-Wa’azi 7:1)

 1. 1. Duk rayuwarmu, A kullum muna so

  Mu riƙa yi wa Jehobah biyayya.

  In muna yin abin Da Allah yake so,

  Za mu faranta Wa Allah rai.

 2. 2. Shaiɗan ya fi so Mu nemi ɗaukaka,

  Har da arziki, A wannan duniyar.

  Amma duk wofi ne, In mun so duniya,

  Ba za mu sami Albarka ba.

 3. 3. Muna so Allah Ya amince da mu

  Domin mu sami Rai na har abada.

  Mu dogara da shi, Mu kāre sunansa,

  Kuma mu riƙe Amincinmu.

(Ka kuma duba Far. 11:4; Mis. 22:1; Mal. 3:16; R. Yoh. 20:15.)