Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 34

Mu Zama Masu Aminci

Ka Zabi Sauti
Mu Zama Masu Aminci
DUBA

(Zabura 26)

 1. 1. Ya Allahna, ka ga amincina.

  Ka ga ibadata da bangaskiyata.

  Ina roƙo ka gwada ni da kyau,

  Domin imanina ya yi ƙarfi sosai.

  (AMSHI)

  Amma ni kam, na ƙudurta cewa

  Zan riƙe aminci dukan rayuwata.

 2. 2. Ba na tarayya da masu ƙarya.

  Ba na son mutanen da ba sa gaskiya.

  Ya Allahna, kar ka halaka ni

  Tare da mutanen da ba sa ƙaunar ka.

  (AMSHI)

  Amma ni kam, na ƙudurta cewa

  Zan riƙe aminci dukan rayuwata.

 3. 3. Ina ƙaunar gidanka, Ya Allah.

  Ina so in riƙa bauta maka kullum.

  Zan zagaya a cikin gidanka

  Don a ɗaukaka ka a dukan ƙasashe.

  (AMSHI)

  Amma ni kam, na ƙudurta cewa

  Zan riƙe aminci dukan rayuwata.

(Ka kuma duba Zab. 25:2.)