Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 3

Jehobah Ne Karfinmu, Begenmu da Kuma Makiyayinmu

Ka Zabi Sauti
Jehobah Ne Karfinmu, Begenmu da Kuma Makiyayinmu
DUBA

(Misalai 14:26)

 1. 1. Ya Jehobah, ka ba mu bege,

  bege mai tamani.

  Mun gode don wannan begen,

  muna yin shelar sa.

  Amma matsalolin rayuwa

  na iya sa mu gaji,

  Kuma mu daina yin ƙwazo

  a yin hidimarka.

  (AMSHI)

  Ƙarfinmu, begenmu,

  makiyayinmu,

  Kana biyan bukatunmu.

  Muna yin wa’azi

  da gaba gaɗi

  don muna dogara da kai.

 2.  2. Ya Jehobah ka taimake mu,

  mu riƙa tunawa

  da dukan alkawuranka

  lokacin wahala.

  Kuma dukan alkawuranka

  za su sa mu yi ƙwazo,

  Domin za su ƙarfafa mu

  mu yi shela sosai.

  (AMSHI)

  Ƙarfinmu, begenmu,

  makiyayinmu,

  Kana biyan bukatunmu.

  Muna yin wa’azi

  da gaba gaɗi

  don muna dogara da kai.

(Ka kuma duba Zab. 72:​13, 14; Mis. 3:​5, 6, 26; Irm. 17:7.)