Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 27

Allah Zai Bayyana ’Ya’yansa

Ka Zabi Sauti
Allah Zai Bayyana ’Ya’yansa
DUBA

(Romawa 8:19)

 1. 1. Allah Jehobah Ubanmu

  Zai tara shafaffu.

  Za su kasance da Kristi

  A cikin Mulkinsa.

  (AMSHI)

  ’Ya’yan Jehobah Allahnmu,

  Tare da Ɗan Allah,

  Za su halaka mugaye,

  Su yi sarauta ma.

 2. 2. Shafaffun da suka rage

  Za su koma sama

  Domin su kasance tare

  Da Ubangijinmu.

  (AMSHI)

  ’Ya’yan Jehobah Allahnmu,

  Tare da Ɗan Allah,

  Za su halaka mugaye,

  Su yi sarauta ma.

 3. 3. Ɗan Allah da shafaffun nan

  Za su yaƙi Shaiɗan.

  Sai su zama sarakuna

  A Mulkin Allahnmu.

  (AMSHI)

  ’Ya’yan Jehobah Allahnmu,

  Tare da Ɗan Allah,

  Za su halaka mugaye,

  Su yi sarauta ma.

(Ka kuma duba Dan. 2:​34, 35; 1 Kor. 15:​51, 52; 1 Tas. 4:​15-17.)