Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 23

Jehobah Ya Soma Sarautarsa

Ka Zabi Sauti
Jehobah Ya Soma Sarautarsa
DUBA

(Ru’ya ta Yohanna 11:15)

 1. 1. Mu yabi Yesu Kristi,

  Don ya soma sarauta.

  Kristi shi ne Sarkin Mulkin Allah.

  Duk mu ta da muryarmu.

  Mu riƙa yabon Allah.

  An ba wa Mai Cetonmu,

  Yesu, sarauta.

  (AMSHI)

  Me Mulkin Allahnmu zai kawo?

  Gaskiya har da adalci.

  Me kuma Mulkin nan zai kawo?

  Rai mai cike da jin daɗi.

  Mu yabi Jehobah Allah,

  Mai ƙauna da aminci.

 2. 2. A yaƙin Armageddon,

  Ɗan Allah ne ja-gora.

  Za a halaka ayyukan Shaiɗan.

  Mu je mu yi wa’azi.

  Mu yi shela ga kowa,

  Don su soma bauta

  wa Allah Jehobah.

  (AMSHI)

  Me Mulkin Allahnmu zai kawo?

  Gaskiya har da adalci.

  Me kuma Mulkin nan zai kawo?

  Rai mai cike da jin daɗi.

  Mu yabi Jehobah Allah,

  Mai ƙauna da aminci.

 3.  3. Muna ƙaunar Sarkinmu,

  Muna yabon sa sosai.

  Allahnmu ne ya naɗa shi sarki.

  Ku bauta wa Jehobah;

  Don ku sami albarka.

  Ba da daɗewa ba

  zai soma sarauta.

  (AMSHI)

  Me Mulkin Allahnmu zai kawo?

  Gaskiya har da adalci.

  Me kuma Mulkin nan zai kawo?

  Rai mai cike da jin daɗi.

  Mu yabi Jehobah Allah,

  Mai ƙauna da aminci.

(Ka kuma duba 2 Sam. 7:22; Dan. 2:44; R. Yoh. 7:15.)