Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 22

Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!

Ka Zabi Sauti
Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!

(Ru’ya ta Yohanna 11:15; 12:10)

 1. 1. Jehobah, ba ka da farko,

  Ba ka da ma ƙarshe.

  Yesu ne ka ba Mulkinka,

  Yana yin nufinka.

  Ka riga ka kafa Mulkin,

  Jin daɗi zai zo duniya.

  (AMSHI)

  Allah mun gode ma,

  Domin ka kafa Mulkinka.

  Ɗanka shi ne Sarki.

  Mun ƙosa “Mulkinka ya zo!”

 2. 2. Mala’iku suna waƙa,

  Suna rera yabo.

  Akwai salama a sammai

  Don an kori Shaiɗan.

  Ka riga ka kafa Mulkin,

  Jin daɗi zai zo duniya.

  (AMSHI)

  Allah mun gode ma,

  Domin ka kafa Mulkinka.

  Ɗanka shi ne Sarki.

  Mun ƙosa “Mulkinka ya zo!”

 3.  3. An kusan halaka Shaiɗan,

  Yana fushi sosai.

  Amma za mu sami ’yanci,

  Duk da masifarsa.

  Ka riga ka kafa Mulkin,

  Jin daɗi zai zo duniya.

  (AMSHI)

  Allah mun gode ma,

  Domin ka kafa Mulkinka.

  Ɗanka shi ne Sarki.

  Mun ƙosa “Mulkinka ya zo!”

(Ka kuma duba Dan. 2:​34, 35; 2 Kor. 4:18.)