Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 20

Ka Ba da Danka Mai Daraja

Ka Zabi Sauti
Ka Ba da Danka Mai Daraja
DUBA

(1 Yohanna 4:9)

 1. 1. Jehobah Ubanmu,

  Da ba mu da bege.

  Amma Ɗanka Yesu

  Ya ba mu bege!

  Za mu bauta maka

  Da dukan ƙarfinmu.

  Za mu yi shelar sa

  Don nufinka ke nan.

  (AMSHI)

  Muna rera yabo

  Don ka ba da Ɗanka.

  Za mu riƙa godiya,

  Domin Ɗanka ya fanshe mu.

 2.  2. Jehobah, jinƙanka,

  Na sa mu ƙaunar ka.

  Muna son sunanka

  Da alherinka.

  Amma fansar Yesu

  Ce alheri babba.

  Ya mutu dominmu.

  Kai ne ka aiko shi.

  (AMSHI)

  Muna rera yabo

  Don ka ba da Ɗanka.

  Za mu riƙa godiya,

  Domin Ɗanka ya fanshe mu.

  (KAMMALAWA)

  Jehobah Ubanmu, duk muna godiya.

  Yabon ka muke yi domin ka aiko Ɗanka.

(Ka kuma duba Yoh. 3:16; 15:13.)